Kotun Majistret mai lamba 58 karshin mai Shari’a, Aminu Gabari ta yi umarnin a tsare Injiniya Mu’azu Magaji Dan Saruaniya a asibitin ‘yan sanda.
Tun da fari dai an gurfanar da Dan Sarauniya ne, bisa zargin bata suna inda akayi zargin ya saki baki a kan gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje.
A zaman kotun na ranar Juma’a, lauyan Dan Sarauniya ya yi suka a kan bukatar masu gabatar da kara wadanda suka roki a karantawa Dan Sarauniyar tuhumar da a ke yi masa, sakamakon baya ji sosai biyo bayan hadari da ya yi.
Yayinda ya ke kwarya-kwaryar hukunci mai shari’a, Aminu Gabari ya ayyana cewar, “Tabbas wanda ya ke da matsalar kunne ba za a karanta masa tuhuma ba, tunda ba zai iya jin abin da a ka karanta ba”.
Sai dai kotun ta yi umarni a tsare shi a asibitin ‘yan sanda zuwa ranar Litinin ko kunnen ya warke, kamar yanda wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya rawaito.