Limamin masallacin Juma’a na hukumar shari’a ta jihar Kano, Malam Haruna Muhammad Bawa ya ce, wajibi ne mu rinka kiyaye hakkokin al’ummar da mu ke gudanar da rayuwa tare da su.
Malam Haruna, ya bayyana hakan ne, yayin da yake yiwa wakilin mu na ‘yan Zazu, Ibrahim Abdullahi Soron Dinki, karin bayanin hudubar da ya gabatar.