Tawagar ‘yan wasan Najeriya na Super Eagles sun dawo gida Najeriya, bayan cire su daga daga gasar cin kofin nahiyar Afirka (AFCON) da ke gudana a kasar Kamaru na shekarar 2021.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa, tawagar ‘yan wasan da jami’an, sun dawo ne ta jirgin haya daga Garoua inda suka buga wasanni hudu a gasar.
Super Eagles sun sauka ne da karfe 1:10 na cikin daren Talata a filin jirgin saman Nnamdi Azikwe da ke Abuja, inda jami’an hukumar kwallon kafar Najeriya NFF suka tarbe su.
Jami’an NFF sun samu jagorancin babban sakataren su Mohammed Sanusi, tare da rakiyar mambobin kwamitin zartarwa na tarayya Yusuf Ahmed da Shehu Dikko.