Mai girman bulaliyar majalisar datijai senator orji urzo kalu (kinbiyan kabi) ya miƙa ta’aziyyar rasuwar tsohon ɗan takarar shugabancin ƙasar bahsir Tofa ga iyalai da gwamnati da kuma al’ummar Jihar Kano, ya bayyana shi a matsayin mutumin kirki kuma cikakken ɗan kishin ƙasa, kuma wanda ya bada gudun mawa sosai gurin cigaban kasa da hadin kan aluma gabaki daya.
Sanarwar ta ƙara da cewa Senator orji urzo kalu ya yi addu’ar Allah ya ji ƙan sa sannan ya bai wa iyalai da abokansa haƙurin rashinsa. A kowanne lokaci yakan bada gudummawa da shawara akan al’umara da suka shafi wannan kasa. Mutum ne mai ra’ayin da babu son zuciya. Ameen.