Yanzu nan Mai girma senator Orji Uzor kalu bulaliayar majalisa datijjai ya gana da mai girma shugaban kasa Muhammadu buhari inda suka tatauna mahiman abubuwa da ya Shafi kasa baki daya.
Daya daga cikin abubuwan da suka tatauna shine matsalar tsaro wanda mai girma shugaban kasa ya nuna matukar damuwar da kuma yi alkawarin kawo karshen matsalar a arewa da kuma kasa baki daya.
Sanan suka dora wajen matsalolin dake cikin jamiyar su Wato APC inda shugaban kasa Yace zaiyi kokarin yin adalci da Kuma saka ido gurin tabatar da adalci a zaben dan Takara a APC.
Senator kalu Yace da karshe sun kare da Shugaban kasa inda ya barshi Cikin koshin lafiya cikin fara a da Jin dadi.