Mai girman bulaliyar majalisar datijai senator orji uzor kalu (kinbiyan kabi) yana miƙa ta’aziyya rasuwar babban mallami Dr ahmad bamba BUK ga iyalan sa da gwamnati da kuma al’ummar Jihar Kano baki daya, ya bayyana shi maragayi Dr ahmad bamba a matsayin mutumin kirki kuma cikakken mallami mai kishin kasa da zaman lafiya, kuma wanda ya bada gudun mawa sosai gurin hadin kai da zaman lafiya a kasa baki daya.
Sanarwar ta ƙara da cewa Senator orji urzo kalu ya yi addu’ar Allah ya ji ƙan sa sanan ya bai wa iyalan sa da mallaman kasa baki daya hakuri wanan babban rashi da akai.